Muhawarar 'yan Republican dake neman takarar shugaban kasa ta dauki sabon salo

'Yan Republican uku dake neman jam'iyyar ta tsayar dasu takarar shugaban kasa: Daga hagu Rubio, na tsakiya Trump da na dama Cruz

Muhawarar baya-bayan nan, ta masu neman a tsayar da su ‘yan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam’iyyar Republican ta dauki wani sabon salo, inda ‘yan takarar suka yi ta ta-da jijiyar wuya a jiya Alhamis.

‘Yan takarar sun yi muhawara ne akan batutwan da suka shafi masu shiga kasar ba bisa ka’ida ba, da tsare-tsaren Amurka akan Gabas ta Tsakiya da kuma yin kididdiga akan kudaden harajin ‘yan takarar.

Hamshakin mai kudin nan Donald Trump, ya kara jaddada aniyarsa da ya gabatar, ta gina katanga a tsakanin Amurka da Mexico, wacce ya ce zai kara tsawon ta da taku goma, saboda adawar da shugabannin Mexico suka nuna kan wannan shiri.

Su kuwa Sanata Marco Rubio da Sanata Ted Cruz, sun zargi Trump da yin amfani da ‘yan cirani wajen gina wasu daga cikin manyan gidajensa.

Sun kara da cewa Trump sai da ya biya Dalar amurka Miliyan daya, saboda yin amfani da ya yi da mutanen da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba wajen gina wasu gidajensa.