Guguwar Maria ta ci gaba da kadawa yau jumma’a da safe da karfin gudun kilomita dari biyu da biyar a awa guda.
Kudu maso gabashin Buhamas ma zai fuskanci guguwar da ta tafka ruwa a Puerto Rico da jamhuriyar Demonican.
Yanzu haka dai guguwar dake da karfin maki uku ta kada Peurto Rico ne da karfin maki hudu ranar Laraba ta sanya ambaliyar ruwa a wurare da dama , ko da yake bata yi barna ainun ba, duk da haka ta shafi wurare da dama a Damonican Republic
Wannan ce guguwa mafi karfi da aka fuskanta a yankin na Peurto Rico dake karkashin Amurka cikin kusan shekaru casa’in. gwamnan yankin Ricardo Rossello yace, akwai bukatar agajin gaggawa a yankin.
Kawo yanzu ba a iya tantance barnar da guguwar tayi ba, kasance har yanzu ba a iya shiga yankin. Sai dai akwai rahotannin dake nuni da cewa, ana fama da ambaliyar ruwa da tabo.