Muguwar gobarar daji ta kusa lakume garin Fort McMurray a kasar Canada

Wani yankin For McMurray da yake ci da wuta

Daukacin jama’ar birnin Fort McMurray da ke Alberta a kasar Canada sun kauracewa birnin sakamakon yaduwar wutar daji mafi muni da aka taba gani a yan shekarun nan.

Kusan mutane Dubu Casa’in ne aka umarta da barin garin, sakamakon yadda ma’aikatan kashe gobara suka kasa dakile wutar daga ci gaba da yaduwa. Babbar hanyar fita daga garin guda daya ce rak.

Sannan kayan sayarwa a shaguna da kayan masarufi da kuma gidajen man da ke kan hanyar suna ta karewa. Zuwa yanzu gine-gine kamar Dari Shida sun kone. Shugaban ma’aikatan kashe gobarar garin Darby Allen ya fada jiya Laraba cewa wannan muguwar wuta ce.

Ya kara da cewa, ba ko ina ne ya kone a garin ba, amma wutar na iya zakulo wuraren ta kuma cinye su. Shima Shugaban kasar Justin Trudeau yace tana da tada hankali, sannan gwamanatin tarayya zata taimaka wa Alberta.

Ba dai rahoton wasu da wutar ta jikkata, amma hukumomi sun dora laifin akan zazzafan yanayi hade da iskar bazara. Alberta dai nan ne babbar ma’ajiyar man fetur din Canada wacce ta uku ce a duniya baya ga Saudiyya da Venezuela.

McMurray, an tanadi wurin da za'a kwashe mutane domin su fita daga garin