Mugabe ya yi Fitar Farko a Bainar Jama'a a Yau Juma'a

Robert Mugabe

Dadadden shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya yi fitowar farko a bainar jama’a a yau Juma’a, tun bayan da sojojin kasar suka masa daurin talala a farko farkon wannan mako.

Mugabe ya isa jami’ar Open a waje babban birnin kasar Harare don halartar taron yaye dalibai a matsayin babban bako.


Rundunar tsaron Zimbabwe ta fitar da hotuna da dama na shugaba Mugabe a jiya alhamis, yayin da aka karanta wata sanarwa ta rundunar sojojoi a kafofin yada labarai na kasar.


Sanarwar tace Rundunar Tsaron Zimbabwe tana wata ganawa da shugaba Mugabe wanda shine babban kwamandan rundunar sojan kasar a kan mataki na gaba, kuma zata shawarci kasar da zarar ta kammala ganawa da shi.


Wasu Karin hotuna sun nuna shugaba Mugabe na ganawa da rukunin masu shiga tsakani daga Afrika ta Kudu da kuma jagororin sojan kasar da suka dage cewar wannan ba juyin mulki ba ne. Kungiyar nan mai karfi da tasiri ta tsoffin sojojin da suka yi yakin kwatar 'yancin Zimbabwe, ta bayyana wannan matakiun da sojoji suka dauka a zaman "gyara ba tare da zubda jinni ba."