"Muddun Babu Gyarar Hanya, To Babu Kada Kuri'a," Inji Mutanen Karkara A Bauchi

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi)

A wani yinkuri na neman samun romon dimokaradiyya, wasu talakawan jihar Bauchi ta arewacin Najeriya, sun yi barazanar kaurace ma kada kuri'a muddun ba a gyara masu hanyoyi kamar yadda aka sha yin masu alkawari ba.

Al’ummomin Kauyuka sama da talatin na Karamar Hukumar Bauchi, ta hedikwatar jihar sun gudanar da Zanga zanga ta lumana, tare da yin Ikirarin cewa ‘Ba Hanya, Ba Zabe, domin nuna rashin jin dadinsu game da rashin ingantattun hanyoyin a kauyukansu.

Masu zanga zangar sun fito ne daga kayukan da su ka hada da Kangere, Munsal Gwaskwaram da kuma Yuguda. Wasu daga cikin jagororin al’ummar, sun fayyace manufar gudanar da zanga-zangar ta lumana. Su na zayyana yadda aka yi ta yin masu alkawura ba tare da cikawa ba.

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Bauchi, Honorabul Danlami Kawule, shi ne dan majalisa mai wakiltar al’ummar yankin a majalisar dokokin Jihar Bauchin, ya ce zai fara ne da lallaminsu, sannan ya bada tabbacin cewa abin da al’umomin ke nema za a samar musu dashi. Ya na mai tabo azurin kwane bangare.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:

Your browser doesn’t support HTML5

12-11-22 Zanga Zangar Nemar Hanya.mp3