Mu Na Son Gwamnatin Najeriya Ta Fitar Da Matsaya Kan Kisan Gilla Ga Sheikh Aisami-Sheikh Bala Lau

Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban JIBWIS

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci gwamnatin Najeriya ta fitar da matsaya kan wadanda a ke tuhuma da hannu a kisan gilla ga babban malamin nan na Islama a Yobe Sheikh Gwani Aisami.

Sheikh Bala Lau na magana ne bayan mika sakon ta’aziyya ga iyalin marigayin wanda ke cikin manyan malaman kungiyar.

Imam Bala Lau ya kara da cewa lamarin ya girgiza kungiyar don irin hanyar da marigayi Sheikh Aisami ya rasa ran sa.

Malamin na Islama ya jaddada cewa daukar matakin yin adalci ga jinin marigayin shi zai karya lagon masu irin wannan dabi’a ta cin amana.

Sheikh Bala Lau ya nuna takaicin yadda wake daya ke neman bata miya a tsakanin jami’an soja wadanda a ka sani da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Marigayi Sheikh Gwani Aisami na gabatar da wa’azi da tallafawa zaman lafiya a yankin da ke farfadowa daga illar Boko Haram.

A wani faifai na wata nasiha da malamin ya gabatar, ya ja hankali a kan yanda lamuran tsaro da tattalin arziki su ka tabarbare a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adama El Hikaya cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Mu Na Son Gwamnatin Najeriya Ta Fitar Da Matsaya Kan Kisan Gilla Ga Sheikh Aisami-Sheikh Bala Lau.mp3