A shirinmu na nishadi a yau mun sami bakuncin mawaki Abubakar Adam Sanda wanda aka fi sani da Mr A sanda, mawakin hip-hop na Hausa wanda ya ce ganin cewar kada a bar mutan karkara a baya a fagen cigaba musamman a harkar waka tare da rashin samun hanyoyin da zasu isar da sakonninsu ya sa ya fara waka.
Matashin mawakin ya ce ganin cewar ‘yan birni sunyi wa mutan kauye gaba ya sa ya fito daga kauyen Sanda, na karamar hukumar Bunkure domin nuna wa al'umma cewar suma zasu iya ba da tasu gudumuwar a fagen cigaban matasa.
Ya kuma kara da cewa matasa na da matsaloli mussamam ma matasa da suka fara wakokin hip-hop mutane na ganin cewar ba salon waka ce ta harshen Hausa ba, sa’annan jama’a na yi musu kallon asararru kasancewar sun zabi fagen waka a matsayin sana’a.
Mr A sanda ya ce babban burinsa a rayuwa shine sakonnin da yake isarwa su iasa wajen wadanda aka yi domin su, kuma mummunar kallo da rashin kyautata musu da jama’a ke yi, ba abinda ya dace bane domin komai na tafiya da zamani ne.
Daga karshe ya bayyana cewa yawancin wadanda ke musu kallon marasa dabi’a na daga cikin wadanda suke dawo daga baya su zama mawaka.
Your browser doesn’t support HTML5