Mourinho: Nafi Kungiyar Manchester Rayuwa Mai Kyau A Gaba

Tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho ya yi watsi da tayin da kungiyar kwallon kafa ta Benfica ta yi masa na ya kasance mata sabon kocin ‘yan wasanta bayan da ta kori kocinta Rui Vitoria.

Kin amincewarsa yasa wasu ke ganin cewar Mourinho yana kwadayin zama kocin wata kulob daga cikin manyan fitattun kungiyoyi da suke nahiyar Turai.

Mourinho ya taba kasancewa mai horar da kungiyar ta Benfica a shekara ta 2000, daga bisani ya barta bayan ya jagorace ta a wasanni tara a gasar Lig na kasar Portugal.

Cikin watan Disambar 2018 ne, Manchester United ta sallami Mourinho daga bakin aiki bayan ya gaza kai kungiyar ga gaci, inda take samun koma baya cikin wasanninta musamman gasar firimiya lig na bana.

A wata hira da ya yi da manema labarai a kwanakin baya Jose Mourinho ya ce, ko baya kocin Manchester United yana da makoma mai kyau kamar
yadda ita ma United tace tana da makoma ba tare da shi ba, inda yanzu haka ta dauko tsohon dan wasanta Ole Gunnar Sloskjaer, a matsayin mai rukon kwarya zuwa karshen kakar wasan bana.