Papa Roma Francis Ya Ayyan Mother Teresa Waliyyiya

Gungun jama'a da suka halarci bikin nada Mother Teresa waliyyiya, Lahadin nan a dandalin St Peters.

Lahadi, Papa Roma Francis ya ayyana marigayiya Mother Teresa a zaman waliyyiya, a wani biki na musamman domin haka, wanda wani bangare ne na tausayawa da jinkai a shekara, da dubun dubatan mutane suka hallarta a a dandalin St Peters.

Mother Tresa wacce a zamanin rayuwarta ta sami lambar yabo ta Nobel,saboda ayyukanta na kula da mafiya tagayyara cikin talakwan a India, da isa Calcutta na India ne ranar 6 ga watan Janairu 1929.

Mother Tresa wacce ba kakkaurar mutum bace, yar asalin kasar Albania, ta bude wuraren ayyukan jinkai da tallafawa marasa karfi afiyeda kasashe 120 a fadin duniya, wadanda mata irinta wadanda suka sadaukar da kawunansu ga coci, da fiyeda 'yan sakai fiyeda milyan daya suke taimakawa, kuma ita kanta ta tafiyarda rayuwarta cikin sauki, mana'ana bata kwadin duniya.

A rasuwarta ranar biyar ga watan satumba ta shekarar 1997, tana da shekaru 87, abunda ta bari shine littafin Bible dinta, da carbi, sai dai ta bar tarihi da ayyukan masu da kyau wadanda zai yi wuya a sami wadanda zasu kwatanta.