Mutane akalla 12 suka rasa rayukkansu, wasu kamar 50 suka sami raunukka a lokacinda wata mota ta abka cikin wata kasuwar baje kaya ta birnin Berlin a kasar Jamus, inda mutane suka taru suna hada-hadar sayayyar Kirsemeti.
WASHINGTON DC —
‘Yansanda sun tabattarda cewa wannan al’amarin ya faru jiya Litnin a kasuwar Wilhelm, inda kuma a nan ne ma aka cafke shi Direban motar.
Wani mutum na biyu da aka samu a cikin wannan jibgegiyar motar ya mutu a nan wurin da abin ya faru, lokacinda ma’aikatan assibiti ke kokarin kai mishi dauki.
Tuni fadar White House ta shugaban Amurka ta la’anci abinda ta kira farmakin da, a bisa dukkan alamu, na ta’addanci” ne.
Sai dai kuma ‘yansandan Jamus basu kira harin a matsayin na “ta’addanci” ba, kuma ministan harakokin cikin gida na Jamus, Thomas de Maiziere, yace har yanzu akwai abubuwa da dama da ba’a fahimta ba dangane da harin da kuma dalilin kawo shi.