Mota mai amfani da Tunanin Mutum Wajen Sarrafa Kanta

FILE - An employee of Toyota Motor Corp., drives automated driving test vehicle during a test drive of Toyota's self-driving technologies in Tokyo. Such cars are one field in which researchers are seeking to expand the limits of machine learning.

Wasu masu bincike a China sun bayyana Mota mai anfani da tunanin dan Adam wajen tuka kanta ba tare da an saka mata hannu ko kafa ba, wadda itace ta farko a China.

Tawagar masu binciken dai sun fito ne daga Jami’ar Nankai, dake Arewa maso Gabashin birnin Tianjin, sun kuma kwashe shekaru biyu suna wannan nazari kafin fitowa da fasahar.

Abin manaki dai baya karewa idan aka duba yadda motar ke amfani da tunanin mutum wajen sarrafa kanta.

Duk wanda zai tuka motar to zai saka wata na’urar haska bayanai a kansa ya shiga cikin motar ya zauna, idan har yayi tunanin kunna motar to zata tashi, zai kuma iya duk abinda yake so da ita kamar tuka motar da yin baya da tsayawa kai harma kasheta da rufeta duk batare da ya yi amfani da hannuwansa ko kafarsa ba.

Zhang Zhao daya daga cikin masu binciken ya fadawa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa, cikin kayan aikin da aka sakawa motar a kwai na'urorin haska bayanai har 16, da zasu hasko bayanai cikin kwakwalwar mutum. Sun kuma kirkiri wata manhaja da zata fassara bayyanan ta kuma gayawa motar abinda zatayi.

Shima farfesan da ya jagoranci wannan bincike mai suna Duan Feng, cewa ya yi ankirkiri fasahar ne domin taimakawa al'umma, kuma bada dadewa ba za’a iya hada fasahar nan da ta mota maras matuki kamar wadda kamfanin Google yakera domin amfanar jama’a.