Dan wasan gaba na Liverpool dan kasar Masar Mohammad Salah, ya ce yana da karfin guiwar cewar zai samu damar fafatawa a gasar cin kofin duniya na 2018 da za'ayi a kasar Rasha.
Dan wasan ya fadi hakanne sakamakon raunin da ya samu a kafadarsa a wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai na bana tsakanin kulob dinsa Liverpool da Real Madrid, wanda aka doke Liverpool da kwallaye 3-,1 hakan yasa Real Madrid ta lashe a karo na 13.
Mohammad Salah ya fice daga filin cikin kuka bayan sun yi karo da Kaftindin Real Madrid Sergio Ramos, wanda ya kai shi kasa a mintuna na 26 da fara wasa. hakan ya sanya Adam Lallana ya maye gurbinsa a lokacin inda wasu jama'a ke ganin dan wasan bazai samu damar buga wa kasarsa ta Masar wasan kofin duniya da za'ayi a watan Yuni 2018 ba.
Hukumar dake kula da wasannin kwallon Kafa ta kasar Masar ta ce bisa bincike da aka yi kan raunin da dan wasan ya samu a kafadar hannunsa ya nuna cewar dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa zai samu lafiyar da zai buga wasan.
Kasar ta Masar dai zata buga wasan rukuninta na farko ne a gasar ta cin kofin duniya ranar 15 ga watan yuni 2018 tsakaninta da Uruguay.
Salah ya kasance dan wasan da ya zurara kwallaye har guda 44 a wasanni daban daban da ya buga wa kungiyarsa ta Liverpool, haka kuma ya taimaka wa kasarsa ta Masar ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Rasha a bana.
Your browser doesn’t support HTML5