WASHINGTON D.C. —
Shahararran dan wasan kasar Armenia ba zai buga karawar da za su yi da Chelsea ba, yayin da kungiyar ta Arsenal ba ta saka shi a cikin tawagar ‘yan wasan da za su buga wasa a Baku ba.
Henrikh Mkhitaryan, ba zai buga wasan karshe na Europa League ba, yayin da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yanke shawarar cewa ba za ta saka dan wasan a cikin tawagar ‘yan wasan da za su kara da kulab din na Chelsea ba.
An jima ana nuna rashin tabbas kan batun saka dan wasan mai shekaru 30 da haihuwa a cikin taron baje ‘yan wasan.
Rikicin siyasa tsakanin kasarsa ta haihuwa da Azerbaijan ya sa ana nuna shakku kan tsaron lafiyarsa.