Musulmi Sufaye na kasar Masar sun ce za su cigaba da shirye-shiryen bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad kamar yadda suka saba kowace shekara, duk kuwa da matukar bacin ran da ya game kasar, sanadiyyar mummunan harin nan da aka kai wani masallacin Sinai wanda ya yi sanadin mutuwar masu ibada wajen 305 baya ga wasu 128.
Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin na ranar Jumma’a, wanda da dama a Masar ke ganin an kaddamar a Masallacin na Al-Rawdah ne saboda Sufaye na salla a wani masallacin na Al-Rawdah da ke wani kauye mai irin wannan sunan. Sufaye dai sun yadda da sufanci, abin da ya sa wasu masu tsattsauran ra’ayin Islama ke masu ganin batattu.
Sufayen dai sun ce za su yi bukin mauludi ranar Jumma’a mai zuwa a fadin kasar, da kuma Masallacin Al-Hussein da ke Al-Khahira, daya daga cikin masallatai mafiya tsarki a Masar.
Kamar yadda Shugaba Abdel Fattah el-Sissi ya bayar da umurnin a yi, Kasar ta Masar na makokin kwanki uku, saboda kashe-kashen da aka yi dab da lokacin da limamin zai fara huduba.
A wani jawabinsa da aka yada ta gidan talabijin, Shugaban na Masar ya sha alwashin yin amfani da matukar karfin soji kan wadanda su ka kai harin; wadanda su ka tsere daga masallacin yayin da suke ta bude wuta kan motocin agaji da su ka fara isowa don su taimaki wadanda harin ya rutsa da su.
‘Yan sa’o’i bayan jawabin na Sissi, sojojin Masar sun ce wasu jiragen yaki samfurin jet sun kai hari kan ‘yan ta’addan inda su ka gano da dama daga cikin motocin da aka kai harin ta’addancin da su.