Ministan Wasannin Najeriya Ya Bada Umarnin Biyan 'Yan Wasa Alawus Din Su

'Yan Wasan Super Eagles

Ministan matasa da wasanni na Najeriya, Solomon Dalung, ya bayarda umurnin a biya dukkan kudaden alawus na ‘yan wasan Eagles da zasu wakilci Najeriya a wasannin Olympics. An ce kudaden alawus na ‘yan wasan yak are kwata kwata a wurin da suke buga gasar cin kofin kasashen Afirka na matasa ‘yan kasa da shekara 23 a kasar Senegal yanzu haka.

A ranar laraba, ‘yan wasan na Najeriya sun dage suka doke Senegal mai masaukin baki da ci 1 da babu, suka samu hayewa zuwa ga wasan karshe, suka kuma tabbatar da cewa zasu wakilci Afirka a wasannin Olympics na 2016. Gobe asabar zasu yi kokarin lashe wannan kofi a karawar da zasu yi da ‘yan wasan kasar Aljeriya.

Ministan wasanni Dalung yace ya bayyana takaicin cewa tun da aka fara wannan gasa a kasar Senegal, babu wani dan wasa ko kuma jami’insu da ya samu ko sisin kwabo na kudaden alawus dinsu.

Dalung yace wannan wannan wata matsalar gaggawa ce da muka gada. Amma yace ya umurci babban sakatare da darekta janar da su samo kudaden gaggawa domina biya ‘yan wasan kafin gobe asabar.

Yace za a tura wata tawaga ta hukumar wasanni ta klasa ta Najeriya zuwa Senegal domin karfafa guiwar ‘yan wasan a karawar karshe da zasu yi gobe asabar da Aljeriya.