A wata hira da wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibrin, Ministan yace ko kadan ba haka yake nufi ba, kuma abin takaici ne domin ba a baiwa ‘yan Najeriya cikakken abin da ya faru ba. duk da yake yayi hirar ne kimanin watanni hudu da suka gabata, lokacin da yake mayar da martani kan cewa ko Najeriya zata iya daukar nauyin wasan duniya nan gaba ko wata kasa a Afirka.
Wajen amsa wannan tambaya ne Ministan yace har yanzu dai zai yi wuya ga kasashen Afirka, domin matakan samun izinin daukar nauyin wasan suna da wuya.
A cewar Solomon Dalung, ba a yiwa mutane adalci ba wajen daukar wani bangare na maganar aka yada. Ya kuma bayyana cewa yanzu haka sun riga sun yi shirin zuwa buga wasan duniya da za gudanar a Rasha, inda suka tabbatar da cewa sun zabi duk wadanda suka cancanta kuma zasu bayar da gudunmawarsu a wasan.
Gwamnatin Najeriya tana goyon bayan kungiyar Super Eagles, tare da daukar duk matakan da suka kamata na ganin cewa Najeriya ta dawo da martabar ta.
Your browser doesn’t support HTML5