Ministan Matasa da Wasannin Najeriya, Mr. Sunday Dare,, ya yi alkawarin inganta wasan Damben Gargajiya (Traditional Boxing) domin shiga da yin dai-daito da sauran wasanni a kasar.
Mr. Dare, ya bayyana hakanne a yayin da shuwagabannin kungiyar Dambe ta kasa suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata da ta gabata, inda da ya yabawa wadanda suka kafa kungiyar Dambe, saboda daukar wannan wasan zuwa sauran sassan kasar, wanda hakan abin a yaba ne kwarai.
Ministan wanda ya bayyana muhimancin wasan Dambe a kasar Hausa, da cewar shi ne wasa mafi ban sha'awa a Arewacin kasar don nishadi.
Inda kuma ya ba da tabbacin cewa za a shigo da wasan Dambe cikin tsarin wasannin gargajiya, don kirkiro tsari da kawo fa'ida a wasan.
Ya ce, "Yanzu ana da damar da za'a saka jari a cikin matasanmu, ta hanyar yin gwagwarmaya don haka za'a kawo Dambe a cikin wasannin gargajiya a kasa."
Dambe zai tallafa wajen samun aiki ga Matasa, don yaki da zaman kashe wando musanman wadanda suka kafa kungiyar Matasan.