Sai dai masu sa ido akan al’amuran siyasa dana tsaro sun sha bayyana fargabar samun cin zarafin ‘yancin bil’adama da ka iya tasowa daga cikin irin wadannan kungiyoyin sa kan. Sannan wasu jama’ar ma na ganin har sharri akan yiwa mutumin da ka iya kasancewa baya jituwa da wasunsu.
Akwai masu tunanin idan aka gama yaki da Boko Haram ya za a yi da daruruwan matasan da suke gani su kam sun sami abin yin a yaki da ta’addanci? Bincike ya nuna cewa da yawa daga irin wadannan kungiyoyin sa kan a kasashen duniya sun sha rikidewa su zama ‘yan ta’adda in suka yi karfi.
Kwatsam sai ga babban Ministan harkokin Najeriya Birgadiya Janar Mansur Muhammed Dan Ali mai ritaya a kwanaki biyu da suka wuce ya ziyarci jihohin Borno da Yobe masu fama da matsalar rashin tsaro. inda ya tabbatarwa da Wakilinmu abinda ya kai shi jihohin biyu.
Bayan jawabin da ya nuna na neman ganin irin ayyukan da sojojinsu suke yi a wuraren, sai kuma ya yi alnishir da cewa, zasu yi iya kokarinsu na bawa ‘yan bangar sa kan damar rikidasu zuwa daukarsu a aikin sojan kasar don ci gaba da magance rashin tsaro a Najeriya. Ga cikakken rahoton Wakilinmu a Borno, Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5