Yayin da cutar coronavirus ke lakume rayukan jama'a a fadin duniya gwamnatin Najeriya na ci gaba da ɗaukar matakan rage cunkoso a gidajen yari na ƙasar don tabbatar da cewa annobar ba ta shiga gidajen yarin ba. Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci gwamnatocin jihohi su ma su bi sahunsa, dalili kenan da ya sa aka iya sako ɗaruruwan fursunoni a kwanan nan.
Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, ya yi ƙarin haske dangane da dokokin da Shugaba Buhari ya rattaba wa hannu don tabbatar da doka ta bada ikon da za a rage cunkuso a gidajen yarin, wanda a tarihi ba a taɓa samun irinsa ba.
Ministan ya fadi cewa gwamnatin Najeriya ta dauki ingantattun matakan rage cunkoso, ciki har da dokar da ke da nasaba da gidajen yari wadda aka yi wa kwaskwarima ta yadda za a kawar da matsalolin da ke yawaita kange mutane a gidan yari ba tare da ka'ida ba.
Ya kuma ce a baya, hukumomin gidan yari ba su da damar ƙin karɓar mutum idan an kawo shi, amma yanzu sabon tsarin bai yarda ba. An kuma ɗauki matakai da dama don ganin cewa waɗanda suke ɗaure a gidan yari ba tare da an bi ba’asin shari’arsu ba, da adadinsu ya zarta kusan kashi hamsin, an gagguta bin shari'o'in.
"Mata masu juna biyu da kuma masu shayarwa waɗanda ake zargin sun aikata laifuka marasa tsanani, an ɗauki matakin sakin su hakazalika wadanda suka wuce shekara sittin da haihuwa da laifukansu basu taka kara sun karya ba," a cewar ministan. Amma waɗanda ake zargi da aikata manyan laifuka,ciki har da ta’addanci da fashi da makami matakin bai shafesu ba.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5