Ministan Lafiya Na Nijer Ya Yi Bayani Bayan Kamalla Ziyarar Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira A Diffa

Wakiliyar sashin nahiyar Afirka ta majalisar dinkin duniya mai kula da kiwon lafiya tare da ministan lafiya na jamhurira Nijer, Dr Idi Kalla Mainasara sun kammala ziyara domin ganewa idanunsu yadda harkokin kiwon lafiya ke gudana a sansanonin ‘yan gudun hijra dake diffa.

Da yake jawabi ga manema labarai, ministan kiwon lafiya na jamhuriyar Nijer, Dr Idi Mainasara, ya bayyana cewa sun taradda likitoci na aiwatar da ayyukasu kamar yadda ya kamata, kuma duk magungunan da kungiyoyi masu kai tallafi ke aikawa sun isa babu wata tangarda.

Ministan ya kara da cewa likitocin dake ayyukan bada agaji na yin iya bakin kokarin kokarinsu wajan tallafawa ‘yan gudun hijirar da matsalar boko haram ta raba da muhallansu. Ya kuma bayyana cewa duk na’urorin kiwon lafiya da suka sami matsala, gwamnati zata yi iya bakin kokarinta wajan tabbatar da shawo kan lamarin.

Daga karshe ministan ya ce sun karawa likitoci da sauran maikatan agaji a sansanonin kwarin gwiwa musamman yadda aikin da suke yi, aiki ne da Allah ne kadai zai iya biyansu.

Ga rahoton Haruna Mamane Bako daga Jamhuriyar Nijer.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Lafiya Na Nijer Ya Yi Bayani Bayan Kamalla Ziyarar Sansanonin ‘Yan Gudun Jijira A Diffa