Ministan Kudin Ghana ya gabatar da bitar kasafin kudin tsakiyar shekara ga Majalisar Dokoki
Ministan harkokin kudin, Ken Ofori-Atta, ya gabatar da bitar kasafin kudin tsakiyar shekarar 2022 din ne ga majalisar dokoki, kamar yadda Dokar Kuɗin Jama'a ta shekarar 2016 (Doka ta 921) ta nuna. Ministan ya bayyana manufofin tattalin arziki na gwamnati da karin kiyasi na shekarar 2022 da kuma yadda gwamnati ke kokarin magance matsalolin da suka shafi tattalin arzikin da kasar ke fuskanta kwanan nan. Haka kuma a karon farko, Ministan ya yi bayanin hukuncin da gwamnati ta dauka na neman tallafin asusun lamuni na kasa da kasa.
Ministan harkokin kudi ya bayyana dalilin da ya sa gwamnati ta dauki matakin neman tallafin asusun lamuni na kasa da kasa ko IMF a takaice, wanda ya ce wani ma'auni ne na gajeren lokaci, domin duk da abin da “muka kaddara a baya, na wani dan gajeren lokaci domin tallafa wa daidaiton biyan kudadenmu ne. Amma, a dogon zango kuma abin da muke bukata shi ne babban sauyi a tsarin tattalin arzikinmu.
Ya ce, ababen takaici da suka auku a duniya, shekaru biyu da suka wuce na bayyana annobar covid 19 da yakin Rasha da Ukraine suka kawo sauyi a shirye-shiryensu.
Masu amfani da babbar hanyar Accra zuwa Tema za su fara biyan kudade bayan an kammala ayyukan fadada hanyar. Ministan ya ce za a yi amfani da kudaden wajen biyan masu ba da lamuni da samun kudaden shiga. Kuma, gwamnati ba za ta soke tsarin nan na ilmin babban sakandare kyauta ba. Kamar yadda ministan yace, “Ya zuwa yanzu, gwamnati ta kashe kudi dala biliyan 5.3 a shirin, kuma wadanda suka ci gajiyar sun kai kimanin yara miliyan 1.26 a fadin kasar.
Sai dai marasa rinjaye sun sanarwa manema labarai bayan kammala jawabin ministan cewa wannan bitar kasafin kudin ba zai tabuka komai ba domin tattalin arzikin Ghana ba ya hannun da ya dace. Casiel Ato Forson, mamban kwamitin harkokin a majalisar dokoki ne ya yi Magana a madadin marasa rinjayen. Yace, gwamnati ta sa Bankin Ghana ta buga kudi GHC biliyan 22 ba da sanin majalisar dokoki ba, wanda ya sa hauhawan tsadar kaya da ake fama da shi.
Su kuma a nasu bangaren, masu rinjaye a majalisar dokoki, wanda mataimakin shugaban masu rinjayen majalisa, Hon. Afenyo Markins ya yi Magana a madadinsu suka ce, gwamnatin NPP ta cika duk alkawuran da dauka, kuma gwamnati ba ta saka wani haraji ga jama’a ba tunda ta hau gwamnati sai harajin e-levy.
Masanin tattalin arziki, Hamza Adam Attijjany da yake fashin baki ga Muryar Amurka ya nuna cewa ya kamata gwamanti ta yi bayani kan basussukan da ake bin Ghana, kuma yarjejeniyar da Ghana za ta shiga da IMF na dala biliyan 2; yaushe za a samu wadannan kudaden? Sannan kuma ya shawarci gwamnati da ta soke ilmin babban sakandare kyauta ko kuma ta rage wasu nauyin dake kanta.
Saurari rahoton Idris Abdullahi:
Your browser doesn’t support HTML5