Jiya Mohammad Ghabban, ministan harkokin cikin gida na Iraqi ya mikawa mataimakinsa ragamar mulkin ma'aikatar har sai lokacin da Firayim Ministan kasar Haider al-Abadi ya amince.
Baicin ministan cikin gidan, jama'ar kasar sun nuna fushinsu da Firayim Ministan bayan da harin farko ya lakume rayuka dari da saba'in da biyar.
Kawo yanzu masu aikin ceto na cigaba da yin aiki a wurin da bamabamai suka fashe a yankin Karrade suna neman wadanda har yanzu sun bace ba'a gansu ba kuma ba'a ga gawarwakinsu ba. Wadannan hare haren su ne mafi muni tun harin da Amurka ta kai kan babban birnin kasar a shekarar 2003.
Kungiyar ISIS tuni ta dauki alhakin hare-haren tare da cewa ta auna hare-haren ne kan mabiya darkar Shiya.
Hare haren sun auku ne yayinda aka kusa kawo karshen azumi da al'ummar musulmi ke yi a watan Ramadan, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya take zaton ba za'a samu ta'adanci ba kamar yadda jakadan majalisar a Iraqi, Jan Kubis ya yi zato.
Amurka da wasu kasashe 55 sun yi yarjejeniyar tuntubar juna da bayanan asiri akan ta'adanci da zummar kawo karshen irin wannan danyen aikin da yanzu suka ce anfani da karfin soji kadai bai isa ba.