Ministan Cikin Gidan Nijer Bazoum Mohammed Ya Je Yankin Azawak

Ministan cikin gidan Nijer Bazoum Mohamed ya jagoranci wani taro a garin Azeye dake cikin gundumar Abalak a jihar Tahoua, a kan tsaron kasa, zaman lafiya da yaki da kaurar matasa zuwa kasashen waje da kuma kwararar bakin haure duk

Bayan gundumar Birnin N'Konni, ministan cikin gida mai kula da tsaro, Bazoum Mohamed, ya kai ziyara yankin Azawak dake garin Azeye inda ya jagoranci taron samar da tsaro da zaman lafiya a yankin da ya hada jihohin Tahoua da na Agadez.

Taron, ya sami halartar ‘yan majallisun dokoki na kasa da suka fito daga jihohin Agadez da Tahoua, da sarakunan gargajiya na wannan yankin, da gwamnonin wadannan jihohin, da masu fada aji duk a wannan yakin da ma sauran mambobin gwamnatin kasar.

Ministan tsaron na Nijer, a lokacin da yake yiwa mahalarta taron jawabi game da zaman lafiya a wannan yankin da duk fadin kasar a daidai lokacin da tsaro ke kasancewa babban kalubale ga hukumomi da ma al'ummomin jamhuriyar Nijer ya ce. “duk da kasancewar rashin kyawun yanayi, yankin Azawak ya nisanta da wadansu lamura da muke gani a wadansu yankunan kasar mu.

Minista Bazum ya kuma ce harkar tsaro harkar al'umma ce, da zarar al'umma ta ki miyagun dabi'u to zaman lafiya zai dawwama kamar yadda yake a wannan yankin na Azawak a halin yanzu, ya ce ya zama dole a yabawa al’ummar wannan yankin.

Shi kuma, honorable Yasinee Mohamed, dan majalisar dokoki na kasa da ya fito daga wannan yankin cewa yayi, “da'ira Azeye ce ta shirya wannan taron zaman lafiyar, domin kara dawwamar da zaman lafiya a yankin Azawak kuma zasu fadada abin zuwa sauran da'irorin yankin domin zaman yana da kyawu, kuma tabbas akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Azawak.”

Suma, mahalarta taron na zaman lafiya da ministan cikin gida ya jagoranta a garin Azeye, sun gabatar da bukatocin su.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Cikin Gidan Nijer Bazoum Mohammed Ya Je Yankin Azawak - 3'42"