Ministan ya gana da shugaban gwamnatin Kamaru kuma firayim ministan kasar Mr. Philimon Yan a ofishinsa dake Yaounde fadar gwamnatin.
Sun yi tattaunawa kan yadda 'yan gudun hijira daga Najeriya suke a arewacin kasar ta Kamaru, musamman a kauyen Minawawa a jihar arewa mai nisa.
Yawancin 'yan gudun hijiran sun fito ne daga jihohin arewa maso gabas musamman ma daga jihar Adamawa da Borno. Alkalumma sun nuna cewa 'yan Najeriya kusan dubu 40 zuwa 50 ne suke jibge a kauyan. Kimanin dubu 18 maza ne.
Bayan sun kammala tattaunawarsu ministan da tawagarsa da firayim ministan suka ziyarci ministan cikin gidan Kamaru Rene Emmanuel Sabi inda suka sadu da ministan kasashen ketare na Kamaru tare da babban kwamishanan 'yansandan kasar.
Sun tattauna akan yadda Najeriya da Kamaru zasu hada karfi da karfe su mayar da 'yan gudun hijiran ya da yakin Boko Haram ya daidaita kasarsu ta Najeriya.
Dambazau ya yabawa kasar Kamaru domin kokarin da ta yi domin karbar 'yan gudun hijiran daga Najeriya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5