Ministan Birnin Abuja ya sa an tsare wani dan jarida a kan zargin wai ya bata masa suna.
WASHINGTON, DC —
Ministan Birnin Abuja Sanato Bala Mohammed ya sa an tsare wani dan jarida wanda yana zaune a Kaduna.
Rahotanni sun ce 'yan sandan ciki ne suka je Kaduna suka kama Tukur Mamu mawallafin jaridar Zahira suka tafi da shi Abuja bisa ga umurnin wani kotun majistret inda Sanato Bala Mohammed ya shigar da karar cewa dan talikin ya bata masa suna. Lamarin ya jawo 'yan jarida na cikin Najeriya da waje nuna damuwa sabili da cigaba da tsare Tukur Mamu. Sun damu kuma da yadda wasu ke yin anfani da matsayinsu ko mukaminsu wajen takurawa 'yan jarida.
A WANI sanarwar da ta fitar kungiyar 'yan jarida nagari na kowa ta nuna damuwarta da cigaba da tsare dan jaridan. Haka ita ma hadakar kare mutunci aikin jarida ta duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta tsawatar dangane da wannan batu. Shugaban kare hakin 'yan jarida ta Afirka Adamu Abubakar Gwarzo ya ce 'yansanda sun karya doka domin ba zaka kama mutum ba ka sa shi wurin da ake tsare 'yan ta'ada domin shi ba dan ta'adda ba ne. Ya ce akwai abun da shi ministan yake boyewa shi ya sa baya son Tukur Mamu ya buga littafinsa.
Masu kula da harkokin yau da kullum sun ce kama Mamu ba zai rasa nasaba da wani littafi da ya rubuta ba inda ya tabo wata badakala a birnin Abuja.
Duk da dokar bada bayanai har yanzu 'yan jarida na samun matsala wurin samun bayanai daga jami'an gwamnati.
Kungiyar kare hakin 'yan jarida zata yi taro nan da kwana biyar a Faransa domin faduwar da Tukur Mamu ya yi a kotu.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5