Miliyoyin Musulmi Daga Fadin Duniya Na Cigaba Da Gudanar Da Sauran Ayyukan Hajji Bayan Tsayuwar Arfa A Kasa Mai Tsarki Ta Saudiyya.

  • Ibrahim Garba

Ana cigaba da sauran ayyukan Hajji bayan Hawan Arfa.

Miliyoyin mahajjata daga sassan duniya na cigaba da gudanar da sauran ayyukan Hajji bayan gudanar da mafi muhimmancin wato Hawan Arfa

Musulmi kusan miliyan biyu daga sassan duniya sun hallara a Saudiyya don aikin Hajji na shekara-shekara, wanda za a yi kwanaki biyar ana yi.

Kasar Iran ta kaurace ma aikin hajjin na wannan shekarar, ta na mai nuni da abin da ta kira, gazawar Saudin da kuma rashin iya aiki daga bangaren jami'an lafiya da na tsaron kasar. A maimakon haka, dinbin 'yan mas'habar Shi'a sun hallara a birni Mai Tsarki na Karbala, don gudanar da madadin aikin na haji.

A lokacin aikin Hajin bara, daruruwan Iraniya na daga cikin mahajjata akalla 2,000 da su ka mutu a wani turmutsitsin da aka yi a birnin Makkah.

Wannan ba shi ne karo na farko da Iran ta kaurace ma aikin Haji ba, to amma wannan na zuwa ne a daidai lokacin da zaman dardar tsakaninta da Saudiyya ya yi tsanani ainon musamman saboda tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Siriya da Yemen, inda Iran da Saudiyya ke goyon bayan bangarori kishiyoyin juna.

Saudiyya ta katse huldar jakadanci da Iran a watan Janairu, bayan da masu zanga-zanga su ka banka wuta ma ofishin jakadancin Saudi da ke Tehran, saboda kashe wani fitaccen Malamin 'yan Shi'a mai suna Sheikh Nimr al-Nimr.