A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman na shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar a yau, an bayyana cewa, aƙalla 'yan Nijeriya miliyan 5 za su ci moriyar shirin ƙwarewa na fasahar dijital.
Hadin gwiwar da kamfanin Microsoft ya ta'allaka ne kan hadin kai, kwarewar aiki da sauya fasalin dijital biyo bayan tattaunawa tsakanin bangarorin biyu karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, da Shugaban Microsoft Brad Smith a farkon shekarar.
Bayan shawarwari masu yawa tare da gwamnati, Microsoft ya gano manyan ginshiƙai guda uku da za su taimaka wajen gina tushe mai ƙarfi don karfafa tattalin arzikin fasahar dijital a Najeriya: haɗin kai, ƙwarewa da sauya fasahar dijital.
Osibanajo ya bayyana cewa, "muna da niyyar ganin wadannan shirye-shiryen suna da matukar tasiri a rayuwar 'yan kasarmu da ke ci gaba kuma an kebe yankuna 6 don bunkasa manyan hanyoyin sadarwar yanar gizo"