Michelle Obama Na Kan Ziyarar Afirka

  • Ibrahim Garba

Michelle Obama da mahaifiyarta Marian Robinson na sauraron Bonita Bennett.

Uwargidan Shugaban Amurka Michelle Obama ta gana da Limamin Kirista Desmond Tutu mai lambar yabon Nobel na zaman lafiya a jiya Alhamis a daidai lokacin da ta ke kammala ziyarar da ta kai Afirka ta Kudu.

Uwargidan Shugaban Amurka Michelle Obama ta gana da Limamin Kirista Desmond Tutu mai lambar yabon Nobel na zaman lafiya a jiya Alhamis a daidai lokacin da ta ke kammala ziyarar da ta kai Afirka ta Kudu.

Sun gana ne a birnin Cape Town. Kodayake an soke shirin Mrs Obama na ziyartar gidan yarin Robben Island, inda aka daure tsohon shugaban Afirka ta kudun Nelson Mandela na tsawon shekaru 18, saboda rashin kyawun yanayi. Kafin nan ma Uwargidan shugaban Amurka din ta gana da Mr. Mandela a gidansa da ke birnin Johannesburg ranar Talata.

Ranar Laraba kuma, Mrs Obama ta karanta wani jawabi mai sosa rai ga wasu ‘yan mata a Majami’ar Regina Mundi mai tarihi, wadda ta kasance wata cibiya ta yaki da bambancin launin fata ta Afirka ta kudu.

Yau Jumma’a ce Uwargidan Shugaban Amurka da ayarinta su ka isa Botswana, a inda su ke shirin tafiya yawon shakatawa a gandun daji a gobe Asabar.

Mrs Obama na kan ziyara c eta tsawon mako guda a Afirka ta Kudu da Botswana don jan hankali kan shigar matasa a harkokin shugabanci, da ilimi da kuma koshin lafiya.