Dan wasan tsakiya na Manchester United, Michael Carrick zai buga wasan san a karshe a kungiyar ranar lahadi a wasan da Manchester zata yi da Watford a filin wasa na Old Trafford bangaren Firimiya lig mako na 38.
Michael Carrick, mai shekaru 36 yazo Manchester united, ne a 2006 shekaru kimanin shekaru 12 kenan, dan wasan zai buga wasa na 463 kenan a kulob din inda zai ajiye takalman wasansa a karshen kakar wasan bana.
Michael Carrick, ya samu nasarar lashe Firimiya lig 5 da kofin zakarun Turai da sauran wasu kofuna da suka hada da FA Cup da Carling Cup. Haka kuma ya kasance Kaftin a kungiyar bayan da Wayne Rooney, ya koma tsohon kulob dinsa ta Everton.
Kocin Manchester United, Jose Mourinho na bukatar Carrick ya shigo tawagar Kwac-kwac a kungiyar ta Manchester bayan ya ajiye takalman sa. Kocin Manchester united, Mourinho ya ce yana jin cewar dan wasan tsakiyarsa Paul Pgoba, zai cigaba da zama a Kungiyar har zuwa kakar wasan badi.
Ana alakanta barin kungiyar da dan wasan zai yi a karshen kakar wasan bana musamman ganin rashin jituwa tsakaninsa da mai horas da kungiyar.
Jaridar (Express) ta ruwaito cewa dan wasan gaba na PSG Neymar, ya yi wata ganawar surri tsakaninsa da mahukuntar kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid, a watan maris 2018, kan yuwar barin sa kasar faransa don komawa kungiyar ta Real Madrid.
Your browser doesn’t support HTML5