Michael Carrick Ya Zamo Sabon Kaftin A Manchester United

Hukumar gudanarwa ta kungiyar kwallon kafa ta Manchester united, ta nada Michael Carrick, a matsayin sabon kaftin din kungiyar, inda ya maye gurbin tsohon jagoran 'yan wasan Wayne Rooney, wanda ya Koma tsohon kulob dinsa Everton, bayan ya shafe shekaru goma sha ukku a kungiyar ta Manchester.

Carrick, mai shekaru 35 da haihuwa kuma haifaffen kasar Ingila, dan wasan tsakiya, wanda ya buga wasanni a kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, tun daga matakin 'yan kasa da shekara 18 har ya kai matsayin babba a kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila.

Michael Carrick, ya buga wasanni a kungiyoyin kwallon kafa daban daban da suke cikin Ingila, wanda suka hada da Westham, Swindon Town, Birmingham City, da Tottenham, sai kuma Manchester united.
Carrick, ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Manchester united, daga Tottenham a shekara ta 2006, inda a yanzu haka ya shafe shekaru 11 a kungiyar ta Manchester, A tsawon zamansa a Manchester, ya buga wasanni 314 ya kuma jefa kwallaye 17 kacal.

Carrick, wanda yake sa riga mai lamba 16 a kungiyar ta Manchester united, ya nuna farin cikinsa da godiya bisa wannan matsayi na jagoran 'yan wasan Manchester united, da aka bashi, yayi kira da takwarorinsa 'yan wasa da su bashi hadin kai domin ciyar da kungiyar gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

Michael Carrick Ya Zamo Sabon Kaftin A Manchester United