Wani rahoto da hukumar kwallon kafa ta Faransa ta fitar, ya bayyana cewa dan wasan kasar Argentina kaftin din kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi, shi ne yafi kowane dan wasan kwallon kafa karbar albashi a duniyar tamola.
In aka hada jimillar kudaden da ‘yan kwallon kafa ke samu daga albashi, da
sauran kudaden shiga wanda suke samu daga tallar da su keyi wa wasu manyan kamfanoni na Allunan hoto da sauran su.
Bin ciken ya nunar da cewar ana biyan Lionel Messi zunzurutun kudi har euro miliyan €130, duk shekara. Wanda yake biye masa shine dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo, inda yake karbar euro miliyan €113, sai Neymar daga PSG a matsayi na uku, yana samun euro miliyan €91.5.
Antoine Griezmann na Atletico Madrid shine dan wasa na hudu yana amsar euro miliyan €44, Gareth Bale na Real Madrid na karbar euro miliyan €40.2, a matsayi na biyar.
Sauran 'yan wasan da suke cikin jerin 'yan wasa ashirin da sukafi karbar kudi a duniyar tamola sune kamar haka: 6) Iniesta €33M, 7) Alexis Sánchez €30.7M, 8) Coutinho €30M, 9) Lavezzi €28.3M, 10) Luis Suárez €28M, 11) Piqué €27M, 12) Toni Kroos €26.3M, 13) Özil €25.8M, 14) Mbappé €25M.
15) Oscar (Shanghai) €24.3M, 16) Agüero €24.3M, 17) De Bruyne €23.5M, 18) Hulk (Shanghai) €23.4M, 19) Paul Pogba €23.3M, 20) Sergio Ramos €23M.