Lionel Messi na Yunkurin Kasancewa dan Wasan la Liga da Yafi Kowa Jefa Kwallaye a Raga

Argentina's Lionel Messi controls the ball past Belgium's Axel Witsel during the World Cup quarterfinal soccer match between Argentina and Belgium at the Estadio Nacional in Brasilia, Brazil, Saturday, July 5, 2014. (AP Photo/Eraldo Peres)

Shahararren dan wasan kwallo Lionel Messi na yunkurin kasancewa dan wasan la liga da yafi kowa jefa kwallaye a raga ranar asabar mai zuwa, duk da cewa kalaman da yayi a kwanakin baya ya jawo zaman dar-dar a filin wasan Camp Nou, lokacin da yace ba lallai bane ya zauna a kungiyarshi ta Barcalona.

A halin yanzu dai, Barcelona na haramar zama mai masaukin baki a lokacin da zata kara da Sevilla Asabar dinnan, kuma maki biyu kacal Real Madrid mai jagorantar teburin la ligan ta baiwa Barca.

A wasanni uku da aka buga a baya, Messi bai ci kwallo ko daya, saboda haka har yanzu kwallaye 250 ne kacal yaci, kuma idan ya samu maki daya, to zaiyi kunnen doki kennan da Telmo Zarra wanda yafi kowani dan kwallo jefa kwallaye a gasar La liga.

Jama’a da yawa ne suke tunanin yadda rayuwar Messi zata kasancewa bayan barin kungiyar da yake yiwa wasa tun yana mai shekaru 13.

Mahaifin Lionel Messi da wakilinsa sunce kar a damu, dan wasan babu inda zai je, kuma hankalinsa a kwance yake a Barcelona.

Your browser doesn’t support HTML5

Lionel Messi da Barcelona 1"00"