Kodayake shugabannin jam'iyyar PDP sun ce taron na Minna bana siyasa ba ne to mms menene manufar taron?
WASHINGTON, DC —
Jam'iyyar PDP ta gudanar da wani babban taro a Minna fadar jihar gwamnatin Neja.
Dr. Goodluck Jonathan ya halarci taron har ma yayi wata ganawa ta siri da manyan sarakunan gargajiya guda takwas a filin jirgin sama a Minna.
Shugaban jam'iyyar Alhaji Adamu Muazu yayi jawabi inda yace jam'iyyarsu jam'iyya ce mai mutunta 'yan Najeriya saboda haka yayi fatan wadanda suka barta zasu koma cikinta.
Shi ma maimasaukin baki gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu ya yiwa 'yanuwansa gwamnonin da suka fita daga PDP zuwa APC shagube. Yace kodayake lokacin neman kuri'a bai yi ba amma zasu shiga koina su bayyanawa 'yan Najeriya abun da PDP tayi kuma zata yi. Yace Allah ya riga ya zabar masu shugaban kasa wato Goodluck Jonathan ko ana so ko ba'a so.
Saidai a nashi jawabin shugaban kasa bai tabo batun kisan gilla da ake yiwa bayin Allah ba a arewa maso gabashin kasar. Haka kuma bai yi bayanin matsayinsa ba a kan ko zai tsaya takara a zabe mai zuwa. Yace taron ba na neman zabe ba ne amma gangamin hadin kai.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5