Me ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Dage Zaben Shugaban Kasa?

Magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Rivers, ranar 12 ga watan Fabrairu, 2019.

‘Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, tun bayan da hukumar zaben kasar ta INEC ta bayyana cewa ta dage zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisu da aka tsara za a yi a yau Asabar.

Da yawa daga cikin ‘yan kasar sun wayi gari ne da jin labarin wanda aka sanar da shi da tsakar daren jiya Juma’a.

Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Mahmud yakubu ne ya bayyana manema labarai shirin dage zaben.

Hukumar ta INEC ta ambaci wasu matsaloli da suka shafi rarraba kayayyakin zabe a matsayin dalilan da ya sa ta dage zaben zuwa 23 ga watan Fabrairu.

Hukumar har ila yau ta dage zaben gwamnoni zuwa 9 ga watan Maris a maimakon 2 ga wata, kamar yadda aka tsara.

Wannan dai ba shi na karon farko da aka dage zabe a Najeriya ba, ko a 2015 ma an dage zabe, bayan da aka bayyana cewa babu cikakken tsaro.

Wannan lamari ya sa ‘yan Najeriya na ta bayyana mabanbantan ra'ayoyi, inda yayin da wasu ke sukar lamarin wasu kuwa cewa matakin ya yi daidai idan har akwai matsalar da aka hango.

Saurari ra’ayoyin da wakilanmu Sani Malumfashi da Ibrahim Abdulaziz suka tattaro mana daga Katsina da Adamawa:

Your browser doesn’t support HTML5

Me ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Dage Zaben Shugaban Kasa? - 6'23"