Me Ya Sa Shoprite Zai Sayar Da Kantunansa Na Najeriya?

Tambarin Shoprite

Katafaren kantin sayar da kayan masarufi da na amfanin gida Shoprite wanda asalinsa na Afirka ta kudu ne, na nazarin janye mafi aksarin kantunansa ko kuma baki dayansu a Najeriya.

Shoprite ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a yau Litinin wacce VOA ta gani. https://bit.ly/2DtTejC.

A cewarsa ya fara wannan nazarin ne sakamakon yadda masu zuba hannayen Jari da dama ke nuna sha'awar sayen kantunansa na Najeriya.

Hakan na zuwa kusan shekaru 15 bayan da Shoprite suka bude shagunansu a kasar wacce ke da tatttalin arziki mafi girma a nahiyar Afirka.

Shoprite ya samar wa 'yan Najeriya akalla 2000 ayyuka kuma yana da kantuna a jihohi da dama a kasar.

Kamfanin mai katuna fiye da 2,900 a Afirka ya ce annobar Coronavirus ta yi tasiri sosai akan harkokin kasuwancinsa.

Rahotanni da dama na nuni da cewa wannan sanarwa ta Shoprite ta Jefa fargaba a zukatan mutane da dama lura da yadda suka samar wa mutane da dama ayyukan yi.

Shoprite ya zamanto daya daga cikin wuraren da matasa da dama kan je don yin hotuna da kuma shakatawa a lokacin bukukuwan sallah ko kirsimeti.