Masu sauraronmu assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku, Da fatan masu azumi an sha ruwa lafiya.
Yau za a ji kashi na biyu kuma na karshe na maimaicin amsar tambayar nan kan dalilan kasashen Mali da Burkina Faso na shirin kulla yarjejeniya da kasar Rasha, da kaurace ma kasar Faranasa; da kuma yadda al’amarin zai kasance?
Masu tambayar, idan an tuna, su ne: Babandi Mamman Bande,
da Tasiu Unguwar Tudu, Damagaram da Issuhu Madatai, da Ali Sarkin yakin Ni'ma, da Shugaba Iliya Maishayi Garkin Daura.
Ga karashin amsar da wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo daga wurin furfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano.
A sha bayani lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5