Me Yasa Filayen Idi Sukayi Yawa Ne?

Sallar Idi a unguwar Obalende, a garin Ikko.

Imam Tukur Adam Abdullahi al-Mannar na Kaduna yayi bayani a kan wannan

Babban Editan Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustaphan Sakkwato ya tattauna da masanin addinin Islama Imam Tukur Adam Abdullahi al-Mannar na Kaduna, a kan yawaitar filayen sallar Idi a wannan zamani da muke ciki.

Hakan na da nasaba ne da bambancin akida ko na ra'ayi, ko kuma da karuwar yawan jama'ar Musulmi?

Your browser doesn’t support HTML5

Me ya kawo yawaitar filayen Idi ne a wannan zamani?-6':07"

Imam Tukur Adam Abdullahi al-Mannar yayi kira ga al'ummar Musulmi da a karfafawa mata guiwa su rika zuwa sallar Idi kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa sallam ya koyar.