Shugaban rundunar Sojan Najeriya, Kenneth Minimah ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai dake kula da harkokin sojin kasa, game da yadda aka kashe Nera Biliyan Daya da aka baiwa sojojin.
WASHINGTON, D.C —
Kenneth Minimah yace “mun samu koma baya, har muka rasa wasu yankuna, harda Mubi, amma muna aiki tukuru domin kwato su.”
“Ina so in tabbatar wa mutanen Najeriya da ma wadanda rigima ya shafa cewa, sojojin Najeriya zasu cigaba da sadaukar da rayukansu, wajen gani an shawo kan matsalar, har mu kwato duka yankunan dake hannun ‘yan ta’adda.
Wakiliyar Muryar Amurka Madinat Dauda, ta tambayi Sanata Bindo Jibrilla, ko sun samu bayanai game da yadda aka kashe kudaden da aka baiwa sojoji?
Sanatan yace “hakika mu majalisa yanzu, kowa ya gaji, domin gaskiya kasar nan, ana cikin wahala, ba Maiduguri ba, idan aka wayi gari, ba’ayi hankali ba, wannan matsala daga nan har Patakwal sai a iya samun wannan matsala.”
Your browser doesn’t support HTML5