Me Ke Haddasa Guguwa? Daga Ina Ta Ke Fitowa? Ina Za Ta?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalama alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku.

Yau za a ji amsar tambaya mai cewa:

"Assalana alaikum voa. Don Allah ku samo mana amsar wannan tambayar. Wai
shin guguwa da take tasowa ta ratsa wasu kasashenmu na duniya, daga ina take tasowa? Mene ne dalilin da yasa take tasowa?
Ina kuma zata je? ko tana da alaka da wannan karamar iska da muke shaka?"


Masu tambayar hadin gwiwa: Alhaji Kari Bage Bajoga da Kawu Mairuwa Bajoga, jahar gomben Najeriya.

Amsoshi

To idan masu tambayar da ma dinbin masu saurare na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a Adamawa, Muhammad Salisu Lado ya samo daga Farfesan Ilimin Yaniya, Abubakar Sadik Umar, na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawar Najeriya. Sai a danna sautin don sauraron cikakken shirin.

To sai a kasance da mu makon gobe don jin kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambaya kan guguwa da ma amsoshin wasu tambayoyin. Yanzu a madadin wanda ke amsa ma na tambayoyin: Farfesa Abubakar Sadik Umar na Jami’ar Modibbo Adama, da ke Yola Jihar Adamawar Najeriya, da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Lado, da wanda ya bayar da umurni, Daniel Browan, da kuma injiniyanmu, Ni Ibrahim Ka-Almasih Garba ke cewa, sai makon goben, idan Allah ya lkai mu. Wassalam.

A yi saurare lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

AMSOSHIN TAMBAYOYI KAN GUGUWA