Yayin da ya ke bayyana aniyar Hukumar Kula Da Bunkasa Masana’antu Ta Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka ma Najeriya wajen inganta tattalin arzikinta wanda faduwar farashin mai ta nakkasa, Mista Philebus ya ce yawan kayan jabu da ke Najeriya ya wuce misali.
Mista Philebus ya ce kamar sauran masu sayayya na kasashen ketare, shi ma mai saye a Najeriya ya na bukatar kayan saye masu karko. Saboda haka, in ji shi, ya kamata a dokokin kasar su zamanto masu karewa da kuma karfafa kyawawan manufofin gina kasa.
Ita ma Hukumar Kula Da Ingancin Kayan Sayarwa Ta Najeriya (SON) tabbatar cewa sama da kashi 85% na kayan sayarwa da ake shigo da su Najeriya jabu ne, kuma mafi yawansu daga kasar China da makamantansu ake shigo da su don samun muguwar riba.
Shugaban hukumar ta SON, Dr. Joseph Odomodu y ace irin wadannan kayan jabun na matukar barazana ga cigaban Najeriya.
Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5