MDD Ta Zargi Eritrea Da Take Hakkin Bil adama

Wani yanki da ke kan iyakokin Eritrea da Ethiopia

Wani jami’in bincike na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi tir da matakin da kasar Eritrea ta dauka na fatattakar masu kokarin morar ‘yan cinsu na dan adam, da kuma masu kokarin morar‘yancinsu na yin addininsu, kamar yadda wani rahoto ya nuna

A rahoton na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya mayar da hankali kan halin da 'yancin dan adam ke ciki, ya nuna yadda ake samun matsalar take hakkin dan adam da yawa wanda ya kunshi kame ‘yan kasa ba bisa ka’ida ba, keta haddin mutum da azabtarwa.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman da ke kula da hakkin dan adam a Eritrea, Daniela Kravets ta nuna rashin jin dadi game da matsayar da gwamnati ta dauka game da ‘yancin addini.

Sai dai jakadan Eritrea a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, Tesfamicael Gerahtu, ya bayyana rahoton a matsayin wanda aka hada shi don cimma wani burin siyasa.

Ya kuma ce rahoton ya kuma kaucewa bayyana irin ci gaban da kasar ta Eritrea ta samu.