MDD Ta Shirya Taron Fadakar da Mata Akan 'Yanci

Taron bitar fadakar da mata akan 'yanci da MDD ta shirya a Yola

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD Ta shirya wa mata taron fadakar ada kawunansu akan 'yancin da za'a ba mata kamar tadda aka bayyana a kudurin MDD din.

Hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta ce batun samarwa mata da yara mata yanci ba yana nufin mata zasu zama daidai da maza ba kamar yadda wasu ke zato sai dai wata dama ce da zata baiwa mata hakki da kwmantata adalci a al'amuransu na Ya'u da kullum.

Babban jami'in dake kula da rayuwar mata na majalisar dinkin duniya Dokta Titus Angu ya bayyana haka a wata ganawa da 'yan jarida a Yola fadar jihar Adamawa don ilimantar da su tanade tanaden kudirin majalisar dinkin duniya na 1325 kan rawar da mata zasu taka wajen wanzar da zaman lafiya, tsaro, adalci da baiwa mata da yara mata hakkinsu don su fadakar da al'uma don su fadakar da jama'a fa'idar kudirin.

Sakatariyar dindindin ta ma'ajkatar kula da mata ta jihar Adamawa Hajiya Maisaratu Bello ta bayyanawa Muryar Amurka muhimmanci 'yan jarida su YI fafatukar nemawa mata hakkinsu don kauda mummunar fahimtar da wasu ke yi wa kudirin dokar wadda a cewar ta za ta baiwa mata damar ba da tasu gudumawar gina kasa ganin da mata na da rinjaye na sama da kashi hamsin na adadin jama'a.

Wasu 'yan jarida mahalarta bitar Michael Musa daraktan tsara shirye shirye na gidan radiyon jihar Adamawa da Mohammadu Auwal na kanfanin dillanci labarai na Najeriya sun bayana dokar da cewa wata gagarumar ci gaba ba ga mata kadai ba amma ga al'umma baki daya ta hanyar damawa da su a duk harkokin rayuwa.

A jihohin arewacin Najeriya hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya, asusun yara na MDD, kungiyar kasashen turai, gwamnatin tarayyar Najeriya sun soma gwajin wannan kudiri na MDD a jihohi Filato, Gombe da Adamawa inda tuni gwamnatin jihar Filato ta rattaba hannu da soma aiki da dokar yayin da majalisun jihohin Gombe da Adamawa kawo yanzu ba su kammala nazarin dokar ba.

Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

MDD Ta Shirya Taron Fadakar da Mata Akan 'Yanci - 3' 08"