Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wacce ake wa lakabi da UNHCR a takaice, ta kaddamar da wani asusun neman tallafin Dala miliyan 621 domin tallafawa kusan ‘yan gudun hijira miliyan daya.
Mutanen da daga cikin wadanda suka tsere daga gidajensu a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, suke neman mafaka a kasashen da ke makwabtaka da su.
Ita dai kasar ta Congo ta kasance daya daga cikin kasashe a nahiyar Afirka da ke fuskantar yanayi mafi muni dangane da halin da ‘yan gudun hijira suka shiga.
“Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankunan kasar, tun bayan da dakarun gwamnati suka kaddanmar da wani farmaki a watan Disamba akan dakarun hadin gwiwa na ADF.” Inji Andrej Mahecic.
Mafi aksarin ‘yan gudun hijirar dai sun tsere ne zuwa Uganda, wacce take rike da akalla mutum dubu 100, sannan wasu dubbai sun tsallaka zuwa Burundi, Rwanda, Tanzania, Zambia da kuma Angola.