Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta bayyana cewar bayan fiye da kananan yara miliyan guda ne suka gudu daga Sudan Ta Kudu sakamakon barkewar tashin hankali, adadin yaran da suka rasa mazaunansu a cikin kasar su ma miliyan daya ne.
WASHINGTON DC —
Daraktar Yanki ta kungiyar kula da lafiyar iyali dake gabashi da kuma kudancin Sudan Leila Pakkala tace , adadin ya nuna karara “Yadda tashin hankalin ya shafi wadanda suka fi rauni a kasar”.
Pakkala ta kara da cewa “Hakika rayuwar manyan goben na fuskantar barazana.”
Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya ko MDD dake kan gaba kan harkokin rigingimum al’umma a Sudan ta Kudu ita kanta tana fuskantar matsalar tallafi.