Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris-Saint German dan kasar Faransa Kylian Mbappe, ya musanta rade radin da akeyi na cewar zai koma kungiyar Real Madrid, da taka leda a kakar wasa mai zuwa inda ya nisanta kansa da wannan batu.
Dan wasn Mbappe ya taimakawa kasarsa Faransa ta lashe kofin duniya da akayi a Rasha shekara ta 2019, haka kuma ya taimakawa kulob din PSG ta daga kofin Lig 1 na faransa a bana, wanda shine karo na shida bayan da ya jefa kwallaye har 3 a ragar Monaco a yayin wasansu na lig.
Matashin dan wasan mai shekaru 20 da haihuwa ya ce a yanzu ba ya tunanin barin kungiyarsa ta PSG don komawa Real, sai dai ya nayi wa Madrid murnar
dawowar tsohon kocinta Zidane karo na biyu.
An dade ana jita-jitar cewa Madrid za ta sayi wasu manyan 'yan wasa, ciki harda Mbappe da dan wasan Chelsea Hazard wanda shi tuni kungiyoyin biyu sun kusan kammala yarjejiniyar sayen shi.