Yayin da al’ummomin da suka yi gudun tsira da rai saboda rikicin kungiyar Boko Haram ke ci gaba da komawa yankunansu yanzu wani batu da ke tasowa shine na gyaran wuraren da aka lalata a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya inda tashin hankalin ya fi kamari.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa wasu kwamitoci irinsu Presidential Initiative Committee da hukumar tada komadar al’ummomin arewa maso gabas, wato North East Development Commission da zimmar tallafa wa wadannan al’ummomi.
To sai dai kuma a jihar Adamawa, al’ummomin da rikicin Boko Haram ya fi shafa a Madagali da Michika, sun koka da cewa su har yanzu ba su ga tasirin wadannan kwamitoci ba.
Honarabul Stephen Madwa, shugaban kungiyar manoma shinkafa, dan asalin yankin Michika, ya ce bayan matakin kandagarkin da gwamnatin jihar Adamawa ke dauka da yanzu sun shiga halin ni ‘yasu musamman a lokacin damina.
Honarabul Abdullahi Adamu Prembe, da ke zama kwamishinan raya karkara da ci gaba, ya bayyana kokarin da gwamnatin jihar ke yi a yanzu, ya kuma ce ayyukan da suke yi a jihar suna kai wa har yankunan karkara
Ya zuwa yanzu, akwai wasu dubban ‘yan gudun hijirar Boko Haram da ke kasar Kamaru, batun da Rabaran Joel Billi, shugaban majami’ar EYN a Najeriya ke kira ga gwamnatocin wadannan jihohi su yi koyi da abinda gwamnatin jihar Borno ke yi.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5