Mamman Mustapha Almu na kungiyar WATAP na cikin jigajigaen zanga zangar wanda ya ce garin Yamai ya mutu saboda gwamnati ta kashewa talakawa wurin sana'o'insu.
Inji Almu jama'ar birnin na fuskantar matsaloli da yawa. Babbar kasuwar birnin an rufeta domin ba harkar siyasa ake yi a kasuwar ba, acewarsa. Inji shi kowa ya matsudomin gwamnatin kasar bata tsinana masu komi ba.
Abdullahi Shalare wani masanin harkokin doka ya bayyana cewa matsalolin suna da yawa. Misali, yace babu adalci kuma babu dimokradiya sai karya da makirci.
Mutanen da aka rusa shagunan da hukumomin Yamai suka yi ya shafa a watan Agustan wannan shekara su ma sun shiga zanga zangar. Hajiya Gambo wadda ta rasa shagon sayar da abinci tace kasuwanci ya mutu. Da tana da shago inda take dafa tuwo tana sayarwa amma yanzu babu. Tace ta koma 'yar maula.
'Yan adawa da suka zargi shugaba Issoufou Muhammadou da gazawa sun karbi goron gayyata na zuwa zanga zangar daga kungiyoyin fararen hula. 'Yan majalisar dokokin kasa na bangaren adawa suna wurin.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5