'Yan gudun hijiran daga bangaren Fulani da sauran kabilun yankunan Kananan Hukumomin Mangu, Bokkos da Barkin Ladi a jahar Filato, sun tsinci kansu a sansanonin biyo bayan hare-haren da ya auku a yankunan nasu, wanda yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi da kona gidajensu.
A wurin wani taron manema labarai da hadaddiyar kungiyoyin Fulani suka kira a cikin garin na Jos, sun koka kan yadda suka shiga halin tashin hankali ba tare da an kula su ba.
Imam Abubakar Isah Ahmad daga garin Bokkos, yace tun a baya da matar Shugaban Kasa ta kawo tallafi, rabon bai kai kansu ba.
yace al'ummarsu, tayi asara da yawa.
Ita kuma Madam Mary Isah dake gudun hijira a cikin garin Bokkos, ta ce suna bukatar abinci, abin kwanciya, tufafi da sauran kayayyaki na bukatun rayuwa na yau da kullum.
Da ya ke bayani, Pastor Iliya Joshua Tat, wanda shima ya ke gudun hijira, yace alkaluman mutane dake gudun hijira a inda yake sun kai dubu goma sha biyar.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta Tsakiya kuma Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, yace nan gaba kadan zasu shirya taro na masu ruwa da tsaki don magance matsalolin tsaro a yankin.
a saurari rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5