Mayakan Kurdawa Sun Kwato Birnin Kobani daga Kungiyar ISIS

Mayakan Kurdawa

Ma'aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon tace yanzu mayakan sakai na kurdawa su suke rike da kimanin kashi 90 cikin dari na binrin Kobani, wanda ya dakushe muhimmin burin kungiyar mayakan sakai ISIS.

Cibiyar kula da harkokin yake yaken Amurka, wacce take jagorancin rundunar taron dangi ta kasa da kasa masu fafatawa da ISIS, tayi barka ga mayakan kurdawan, wadanda tace sunyi yaki tukuru tareda sadaukar da kai, tace sake kama garin Kobani, babban koma baya ne ga ISIS.

Mayakan kurdawan, wadanda jiragen Amurka suke rufawa baya ta wajen kai farmaki sun juma suna fafatawa da mayakan sakan ISIS. Birnin yana daf da kan iyakar Syria da Turkiyya. Kuma duk wanda yake da iko kan binrin, to shi ke da iko kan babbar matsallakar da take yankin.

Amma galibin birnin kusan an lalatashi. Dubban mutane basu da muhalli, inji wani jami'in kurdawa, kuma babu asibitoci, babu ruwa kuma babu abinci.