Mayakan ISIS Sun Kashe Sojojin Iraki 10

  • Ibrahim Garba

Wani barin wuta a lokacin yakin Mosul na kasar Iraki.

Dakarun ISIS sun hallaka wasu jami’an tsaron gwamnatin Iraki 10 da safiyar jiya Asabar, al’amarin da ya janyo fargabar yiwuwar sake dawowar masu ikirarin jahadin a kasar.

Jami’an tsaron Iraki sun fadi a wata takardar bayani cewa harin, wanda aka kai daura da birnin Samara na yankin tsakiyar kasar, shiryayye ne.

Wannan shi ne hari mafi muni cikin tsawon watanni da dama da wasu boyayyun ‘yan ISIS su ka kai, wadanda su kai kai hare hare na sari ka noke kan jami’an tsaro a wuraren da ke lungu a arewaci da kuma yammacin kasar.

A makon jiya ISIS ta yi ikirarin kai wani harin kunar bakin wake wanda ya yi sanadin raunata mutane hudu a wajen wani ofishin jami’an leken asiri a lardin Kirkuk na arewacin kasar.